
Rahotanni daga Filin Idi t a cikin garin Bauchi, sun tabbatar da cewa wani yaro ya rasa ransa a lokacin da ake gudanar da Sallar Jana’izar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Wannan lamari ya tayar da hankali, kasancewar babu wanda ya san daga ina yaron ya fito, ko kuma a hannun wane yake kafin faruwar lamarin.
A Saboda haka, ana roƙon jama’a da su taimaka wajen yada wannan bayani, ko Allah zai sa a gano ‘yan’uwansa.
Gawar yaron tana cibiyar lafiya dake unguwar Bakaro bayan Fada, inda aka kai shi tun bayan mutuwarsa.
Sai dai akwai yiwuwar kai gawar asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake birnin Bauchi

