
Hatsarin mota ya afku Mile 3 Sabuwa da ke nan cikin garin Gombe bayan wata babbar motar ɗaukar kaya Trailer da ta taso daga jihar Taraba ta rasa birki yayin da take shiga yankin.
Direban motar ya yi ƙoƙarin kaucewa domin gujewa haddasa babbar asara, inda ya sauya hanya, sai dai motar ta murƙushe wasu motoci, shaguna da kuma mutane da ke kusa da wajen.
An tabbatar da cewa mutane bakwai motar ta murƙushe, yayin da mutum uku daga cikinsu suka rasu nan take, wasu kuma suka samu raunuka daban-daban, inda jama’a suka yi ta ƙoƙarin ceto waɗanda abin ya shafa tare da kwashe kayayyakin da hatsarin ya lalata.
Allah Ya ji ƙan waɗanda suka rasu, Ya bai wa waɗanda suka samu raunuka lafiya, Ya kuma kiyaye aukuwar irin wannan iftila’i a nan gaba.

