
Jami’ar bayero ta lashe gasar kwallon kwando ta jami’o’in yankin Arewa maso Yamma
A faggen wasanni; Jami’ar Bayero da ke Kano, Bayero University Kano (BUK), ta lashe gasar kwallon kwando ta jami’o’in yankin Arewa maso Yamma karo na uku, wadda aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) gasar da aka kammala a karshen makon da ya gabata.
Gasar ta haɗa manyan jami’o’i daga jihohin Arewa maso Yamma, inda ƙungiyar kwallon kwando ta Jami’ar Bayero Kano ta nuna bajinta da kwarewa, tare da doke abokan hamayyarta har ta kai ga ɗaukar kofin gasar.
Masu shirya gasar sun yabawa Jami’ar Bayero Kano bisa tsari, ladabi da kuma hazakar ‘yan wasanta, inda suka ce nasarar ta nuna yadda wasannin jami’o’i ke ƙara samun ci gaba a yankin.
Nasarar ta BUK ta janyo farin ciki da alfahari ga ɗalibai, malamai da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya, tare da ƙarfafa gwiwar matasa wajen rungumar wasanni a matsayin hanyar ci gaba da haɗin kai.
Wannan nasara na ƙara ɗora Jami’ar Bayero Kano a kan taswirar manyan cibiyoyin wasanni a Najeriya, musamman a fannin kwallon kwando.
ARGT


1 Comment
My phone