
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu tace laifi ne dalibi ya boye matakin karatun da yake
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu JAMB ta bada sanarwar da take nuna cewa daliban da suke manyan makarantu, suma sun iya yin rajista su rubuta jarrabawar ta UTME da wadda za’a gurbin karatu na kai tsaye DE, matukar dai har sun bada bayanin kan halin da suke ciki na karatu.
Hukumar ta ja kunne masu cika fom din duk wadanda basu yi hakan ba, hakan zai sa su damar karatun da suka sabuwa da kuma tsohuwa.
A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun mai ba hukumar shawara,Dakta Fabian Benjamin ya ce ita jarrabawar wurin da ake tura mutum ya ce da akwai wasu da suke yi ma kansu kallon sun san komai dangane da hukumar wanda hakan ya sa wasu sun kasa gane abinda hukumar ta ke nufi akan sanarwar da ta fitar data shafi jarrabawar shekarar 2026 UTME/DE, hakan ya sa iyayen yara da su masu son yin ita jarrabawar suke shiga wani halin da ya daure masu kai.
An ja hankalin hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu kan wadansu abubuwan da ake yi wadanda basu dace ba,irin hakan yana sa wasu su kara shiga cikin halin kaka nikayi kan yadda za su cika fom dinsu kamar yadda ya dace,daga karshe sai irin hakan ta sa a kin umarnin ita Hukumar wadanda za su yi ragistar jarrabawar 2026 UTME/DE,kamar yadda yake a cikin sanarwar da hukumar ta fitar 2026 UTME/DE .
LD

