
Kwadaye da fushi nadaga cikin abubuwan dasuke jefa mutane cikin halaka. Farfesa Aminu Isma’il Sagagi .
Kwadaye da Fushi sune Suke jefa jama’a cikin munana ayyuka musamman a ruyuwar yau da kullun.
Farfesa Aminu Isma’il Sagagi ne yake wannan jawabi a yayin Taron kungiyar Harsashin Musulinci ta Nigeria (Islamic Foundation of Nigeria) da ta gudanar Mai taken ” Da Me Azumin bana zaifi na bara?”
farfesa Aminu yace kwadaye ne yake sawa mutane suke kawo karanci tsaro, cinhaci da rashawa, maganganu na bata, da yida Wani ko annaminci. dakuma Fushi ga Wanda Yankasa mallakan kansa lokacin da aka fusata shi wajan huce guda da iri.
kazalika Farfesa Sagagi yaja hankalin Daukacin Al’ Ummar musulmi dasu maida hankalinsu wajan ibadar azumi kamar yadda manzan Allah sallalahu alaihi wasalam ya gudanar a lokacin Rayuwar sa.
Daga karshe farfesa Aminu Isma’il Sagagi Malami a jami’ar bayaro ya yabawa shugabanin dasuka kafa kungiyar ta Harsashin Musulinci shakara (60) tana gudanar aikin hidimtawa al’ummah musulmi a fadin Kasar Nan da makbatanta.

