
Matashin ɗan siyasa Hon. Musa Sani Indabo ya miƙa takardar sa ta sha’awar neman tsayawa takarar Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Wudil da Garko a jam’iyyar NDC.
A jawabin sa ya bayyana cewa ya fito wannan takara ne sakamakon kiraye-kiraye da matasa maza da mata, lungu da saƙo da suke yi akan ya fito wannan takara shine yaga ya dace ya amsa kiran su.
Inda ya ƙara da cewa “da zarar Allah ya bani wannan dama nayi alƙawarin zan cigaba da riƙe amana tare da karɓar duk shawarwarin da shugabanci yazo da su don cigaban jama’ar ƙananan hukumomin Wudil da Garko da jam’iyyar NDC mai albarka.

