Shugaban Kwamitin Kula da Kwalejojin horar da Jami’an “yan Sanda ja Majalisar Tarayya Kuma Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Ƙananan Hukumomin Fufore da Song Barrister Aliyu Wakili Boya shine ya bayyana hakan lokacin da jaridar Abknews24 take zanyatawa dashi.
Barrister Boya yace sun mika kudurin neman karin makarantun horar da Jami’an yan Sandan har guda 28 Kari akan 25 da ake dasu a Kasar nan.
Yace tuni Shugaban Kasa ya amince dayin hakan a dukkanin shiyoyin da suke yankuna shida na Kasar, wato Arewa Maso yamma da Arewa maso Gabas da Kuma Arewa ta Tsakiya.
Sauran sune kudi Maso Kudu da Kudu da Kudu Maso yamma da Kuma Kudu Maso Gabas.
Shugaban Kwamitin Kula da Kwalejojin horar da Jami’an yan Sandan Barista Boya ya yabawa shugaba Tinubu bisa yadda yake kokarin samar da Tsaro a fadin Kasar Nan
A bangaren samar da ababan more rayuwa kuwa yace a tsawon lokacin da yayi Yana wakinlcin al’umar Kananan Hukumomin Fufore da Song Babu wani Dan Majalisar da ya fishi samawa marasa ayyukan yi, inda yace zuwa yanzu ya dauki marasa aikin Dan Sanda sama da 300 Kuma dukkaninsu a yanzu haka suna sanye da kayan aikinsu domin cigaba da hidimtawa al’umar Kasa.

