
SSS ta gurfanar da wanda ake zargi da shirya harin gidan yarin Kuje da na banki a Edo
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS ta gurfanar da Abdulazeez Obadaki, wanda ake zargi da jagorantar harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje a Abuja a 2022, har ya tsere tare da wasu fursunoni.
An gurfanar da shi gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik kan tuhume-tuhume shida da suka shafi laifukan ta’addanci, ciki har da kasancewa mamba a Ansaru, boye bayanan da za su kai ga kama wani shugaban ‘yan ta’adda, da kitsa hare-haren bankuna hudu a Edo.
A cewar SSS, Obadak, wanda ake kira Bombo, ya karbi N300,000 bayan harin bankuna da aka kai a Uromi, Edo.
Haka kuma ana zarginsa da hada baki wajen shirya harin Kuje wanda ya bai wa kansa da wasu fursunoni damar tserewa.
Obadaki ya amsa laifin tserewa daga halastacciyar tsarewa, amma ya musanta sauran tuhume-tuhume biyar.
Kotun ta dage shari’ar zuwa 26 ga Janairu, 2026, tare da umarnin ci gaba da tsare shi a hannun DSS.

