
Shugaban majalisar dattawa yace basuyi watsi da tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba
Shugaban Majalisar Dattija Godswill Akpabio ya yi ƙarin haske kan gyaran dokar zaɓen ƙasar nan ta shekarar 2022, wadda majalisar ta amince da ita a makon da ya fice.
Amincewa da gyare-gyaren ga dokar ya bar baya da ƙura, inda ƴan adawa da ƙungiyoyi suka riƙa sukar majalisar kan rashin amincewa da gyaran sashen da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi a wurin ƙaddamar da wani littafi a Abuja a ranar Asabar, Godswill Akpabio ya ce ba a haramta tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba, sai dai an cire wurin da aka ce za’a tura sakamakon zaɓen ka-tsaye.
Shugaban yakara da cewa Abin da kawai suka ce shi ne a cire ɓangaren da ya ce ‘kai-tsaye, domin idan aka ce haka to akwai batun matsalar network inda ba za a iya tura saƙo ba.
Mutane da dama na ganin cewa tura sakamakon zaɓe kai-tsaye zai rage maguɗin zaɓe da ake zargin anayi a lokutan zaɓe a faɗin ƙasar nan.
BBC

