Saboda ƴan matana na saci indomie amma ba wacce ta taɓa kawo min ziyara a gidan yari – Matashi
Usama Abdullahi, matashi mai shekaru 24 da aka yanke wa hukunci, ya ce ya saci fakitin indomie domin ‘yan matansa uku, amma babu ko daya daga cikinssu da ta ziyarce shi a kurkuku.
Wannan matashin, wanda ke aiki a wajen wanke motoci a ƙaramar hukumar Shelleng ta jihar Adamawa, ya ce ya gudu zuwa wani gari bayan ya aikata laifin, kafin daga bisani a kama shi.
An yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali na Shelleng saboda satar.
Ya ce: “Na saci Indomie na raba wa ‘yan matana uku.”
“Tun da aka kai ni gidan gyaran hali, babu ɗaya daga cikinsu da ta ziyarce ni. Saboda haka ba zan sake kula su ba idan na fito, ” in ji shi.


Saboda ƴan matana na saci indomie amma ba wacce ta taɓa kawo min ziyara a gidan yari – Matashi