
Innalillahi wainna ilaihir rajiuunn, hakika Rashin Maulanmu Shehu Dahiru Usman Bauchi wani Babban Rashi ne da ya haifar da gibi a Darikar Tijjaniyya da Musulmi baki Daya.
A madadin Shugabannin Ƙungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa Muna kika sakon Ta’aziyyarmu ga iyalai da “yan uwa da Abokan arziki da Shehunnanmu da Malamanmu.
Haka zalika Muna sake muka Ta’aziyyarmu ga Shugaban Kasa da Gwamnoni da Sarakunanmu da Sauran almajirai da Muridai.
Muna afdua’ar Allah ya Gafartawa Shehu Dahiru Usman Bauchi ya jikansa davrahama ya tabbatar dashi a Gidan aljanna madaukakiya.
A madadin Shugaba da Sakataren Ƙungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa Barista Imam Habib Dan Almajiri da Shehu Tasiu Ishaq.
SA hannu.
Sakataren yasa Labarai na Ƙungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa.
Abubakar Balarabe kofar Naisa
27/11/2025

