
Musa Iliyasu Kwankwaso: Shekaru 60 masu albarka
Daga Shehu Mustapha Chaji
Allah Ya albarkaci Jihar Kano da mutane da suka shahara suka daukaka a fannoni daban daban na rayuwa suke kuma bada gudunmawar su domin cigaban Al’umma. Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso yana cikin jerin Kanawa da suka sami daukaka da shahara a fannonin da suka zabar wa kansu dan bada gudunmawar su dan cigaban Jihar Kano da Arewa da Najeriya.
Tarihin dimokaradiyya mu ba zai taba cika ba sai an nakalto tarihin gwagwarmaya da gudunmawar Musa Iliyasu Kwankwaso.
Ya kasance cikin mutanen da suka sa siyasar Kano ta zama ta daman saboda suna kokarin ganin cewa Al’umma na kwasar romon dimokaradiyya da samun ayyukan cigaban Kasa. Ya kuma kwashi shekaru yana sharhi kan harkokin siyasa da lissafin siyasa har hakan yasa wasu ke kiran sa Likitan Siyasar Jihar Kano.
Musa Iliyasu Kwankwaso dan Siyasa ne na kusa da Al’umma kuma ya kasance cikin alamomin dimokaradiyya da samar da shugabanci na gari a Jihar Kano da wajen Jihar.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kwashi tsawon shekaru yana hidima ga Al’umma. Yayi aiki a Ma’aikatar Ruwa na Jihar Kano har ya kai matsayin Mukaddashin Darakta. Ya zama Shugaban Karamar Hukumar Madobi har karo biyu. Ya kuma zama mutumin daya fi dadewa yana rike da mukamin Kwamishina a Jihar Kano. Malam Ibrahim Shekarau ya nada shi Kwamishinan Ayyuka na Musamman daga bisa ni ya canza shi zuwa Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma. Shima Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sake nada shi a Matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma a karo na biyu.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bar tarihin ayyukan cigaban kasa da kawo cigaba a mukaman daya rike. Ya kasance mutumin da a kullum kokarin sa ya gan Al’ummar sa sun sami cigaba. Ya kan kuma fifita bukantun Al’ummar sa kan nasa.
Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso na daban ne cikin yan Siyasa saboda hidima da taimakon Al’umma. Shine dan siyasar da zai baka ba tare da ka tambaya ba. Sannan yana da kokarin sada zumunci da ziyarce ziyarce dan taya murna ko ta’aziyya ko jaje ga yan’uwa da abokai da magoya baya da abokan hulda. Kullum kokarin sa samar da cigaba da taimakon Al’umma.
Kuma salon siyasar Musa Iliyasu Kwankwaso baya siyasa da gaba ko cin mutunci ko tada zaune tsaye. A salon siyasar sa kasancewar yana kusa da na kasa a kullum yana zakulo masu yiwa Jam’iyyar APC hidima yana taimaka musu dan su sami kwarin gwiwar ana sane da kokarin su. Ya kuma fadada wannan kokarin nasa wajen taimakawa masu yada manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Jihar Kano.
Musa Iliyasu Kwankwaso jarumi ne mara tsoro a kokarin sa na ganin an samar da shugabanci na gari da Al’umma su mori romon dimokaradiyya a Jihar Kano.
Ya kuma kasance cikin yan kalilan da suke goyon bayan Shugaba Tinubu saboda fahimtar kyakyawan manufar sa na dora Najeriya a tafarkin cigaba da bunkasar tattalin arziki. Ya kasance cikin masu da’awar tunatar da yan Arewa ayyukan cigaba da Shugaba Tinubu keyi a Jihar Kano da Arewacin Najeriya.
Sarkin Yakin Karaye Mai Murabus ya kasance cikin mutanen da Shugaba Tinubu ya nada su jagoranci Hukumar Kogunan Hadejia da Jama’are. Shugaba Tinubu ya nada Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin Babban Daraktan Kudi na Hukumar. Gogewa da sanin aikin Musa Iliyasu Kwankwaso ya taimaka kwarai wajen ayyukan cigaba da Engr. Rabiu Suleiman Bichi keyi a Hukumar Kogunan Hadejia da Jama’are. Masha Allah, a wannan shekarar ba’a sami ambaliya a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi ba. Kuma Hukumar Hadejia da Jama’are ta zama ta daya a Ma’aikatun Gwamnatin Tarraya da suke Jihar Kano da suka fi biyan Haraji ga Hukumar Haraji ta Kasa a wannan shekarar 2025.
Hon.(Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso ya kafa tarihi wajen bunkasar Jihar Kano a fannonin samar da ayyukan cigaban Kasa da bunkasa da dorewar dimokaradiyya. Yan gwagwarmayar dimokaradiyya da samar da shugabanci na gari zasu cigaba da tallata gwaraza irin sa domin ya zama abin koyi musamman ga matasan mu.
Muna fatan Allah Ya karawa Musa Iliyasu Kwankwaso lafiya da tsawon shekaru da karin daukaka da bunkasar tattalin arziki domin ya cigaba da taimakon Al’umma. Muna yi masa fatan Allah Ya kara masa matsayi da manyan mukamai.
Amb. Shehu Mustapha Chaji

