
“TAKAITACCEN SANARWA”
Dangane da tattaunawar siyasa kan kujerar Mataimakin Gwamnan Kano, an jaddada cewa Murtala Sule Garo ya gina kyakkyawan tarihi na hidima, aminci da tallafawa jama’a a dukkan mukaman da ya rike. Wannan ne ya sa yake samun gagarumin goyon baya da addu’o’i daga al’umma.
An bayyana cewa duk wani yunkuri na dakile wannan goyon baya ba zai haifar da sakamako ba, domin nagartaccen jagoranci mai tausayi da aiki a bayyane shi ne ke jan hankalin jama’a.
Haka kuma, an yaba da hangen nesa na Abba Kabir Yusuf wajen bunkasa jihar, tare da kira ga duk masu ruwa da tsaki su ba da goyon baya ga shugabanci mai anfani ga al’umma.
A karshe, an gode wa magoya baya bisa addu’o’i da goyon bayan su, tare da fatan alheri ga gwamnati da jam’iyyar All Progressives Congress wajen ci gaban kasa.
Barr Salisu Sule “Chawi”
Dan siyasa, mai kishin kasa
08060525236

