
Majalisar Dattawan kasar nan ta nemi a dawo da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane ko sauran laifukan ta’addanci, ba tare da wani zabin tara ba.
a zaman majalisar na larabar nan, Majalisar ta yanke shawarar a gaggauta gyara dokar ta’addanci domin kafa wannan hukunci.
Haka kuma, Majalisar ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake fasalin tsarin tsaron ƙasa domin inganta ayyukan tsaro, tare da tabbatar masa da cewa Majalisar za ta tsaya tsayin-daka wajen yaki da rashin tsaro

