
Alfindiki Ga Kwankwaso: Kada Ka Rudar da Tarihi, Ba Ka Daga Cikin Masu Kafa APC
Babban jigon jam’iyyar APC kuma babban mai taimaka wa Kakakin Majalisar Wakilai, Alhaji Faizu Alfindiki, ya karyata ikirarin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da cewa yana daga cikin masu kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Alfindiki, wanda ya yi wannan jawabi a Kano a karshen mako, ya bayyana cewa babu wani shaidar tarihi da ke nuna Kwankwaso a matsayin wanda ya taka rawar gani wajen kafa jam’iyyar, domin kuwa ba ya cikin jam’iyyun da suka hada gwiwa wajen samar da APC a shekarar 2013.
Ya ce jam’iyyun da suka dunkule suka kafa APC sun hada da CPC karkashin marigayi Janar Muhammadu Buhari, ACN karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, APGA karkashin Sanata Rochas Okorocha, da kuma ANPP karkashin Kashim Shettima, marigayi Bukar Abba Ibrahim, Ibrahim Shekarau da Yariman Bakura.
Alfindiki ya kuma bayyana cewa wasu fitattun ‘yan siyasa kamar Rotimi Amaechi, Aliyu Wamakko, Murtala Nyako da Bukola Saraki ne suka shiga jam’iyyar daga baya a 2014, shekara guda bayan kafa ta da kuma kammala yarjejeniyar hadin gwiwa.
Duk da haka, ya amince cewa shigar Kwankwaso cikin jam’iyyar ya taimaka mata a zaben 2015, inda ya samu kujerar Sanata, mataimakinsa ya zama gwamna, sannan APC ta kwace duka kujerun siyasa a Kano.
Sai dai ya gargade shi da cewa ya kamata ya ci gaba da nuna godiya ga jam’iyyar APC wacce ta sake farfado da siyasar sa a lokacin da ta ke dab da rushewa.

