
jam’iyar APC a jihar Kano ta nada Baffa Babba Dan Agundi da Rabi’u Sulaiman Bichi Matsayin Chairman da Co-Chairman na E-Ragistartion Membership Committee.
Da yake kaddamar da Kwamitin mai mambobi 14 wanda ke karkashin Jagorancin Engineer Rabiu Sulaiman Bichi, shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas yace sauran Mambobin Kwamitin sun hada da Abdul Adamu Fagge da Musa Ali Kachako.
Sauran sune Shafi’u Abdullahi Darma da Ahmad Aruwa da Sunusi Sa’idu Kiru Majidadi da Khalid Ishaq Diso da Auwalu Ubale Minjibir da Fa’iz Alfindiki da Binta Rabi’u Spikin da Umar Muhd Rabiu da Muhd Tudun Wada Tweeter da kuma Aminu Umar Dawakin Kudu a Matsayin Sakatare.
Alhaji Abbas yayi bayanin yadda ayyukan kwaamitin zai kasance tareda jan hankalin Mambobin Kwamintin wajan yin aiki tukuru domin samun nasarar aikin.
yace aikin zai kasance ne dukkan mazabun da suke kananan Hukumomin Jihar 44.

