
Indiyawa maniyyata aikin umra 42 sun mutu sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Madina zuwa Makka a cikin daren Litinin.
Hatsarin ya faru ne da misalin 1:30 na dare agogon Saudiyya, lokacin da wata motar safa dauke da fasinjoji 43 ta yi taho mu gama da wata tankar mai.
Rahotanni sun ce mutum daya ne ya tsira da ransa daga cikin fasinjojin.
Ministan harkokin wajen Indiya Dr. S. Jaishankar ya wallafa a shafinsa na X cewa ofisoshin jakadancin kasar a Riyadh da Jeddah suna bayar da cikakken tallafi ga Indiyawan da hatsarin ya rusta da su.
Ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan’uwan wadanda suka mutu.

