
Al’ummar unguwar Gobirawa da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano sun roƙi ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini, da ya taimaka wajen kammala aikin titin da aka fara daga Kurna Farin Bene zuwa Babban Layi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa aikin titin wanda Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, yafara amma har yanzu ba a kai ga kammala shi ba, lamarin da suke ganin yana ci gaba da jefa al’umma cikin wahalhalu musamman a lokacin damina.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce titin na da matuƙar muhimmanci ga harkokin sufuri da kasuwanci, kasancewar yana haɗa unguwanni da dama tare da sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma a yankin Gobirawa da kewaye.
Sun ce dalilin roƙon nasu ga Hon. Aliyu Sani Madakin Gini shi ne ganin irin ayyukan alheri da yake gudanarwa a mazaɓarsa, musamman yadda ya shimfiɗa tituna a yankin Kurna Yan Ganda, aikin da suka bayyana a matsayin wanda ya kawo sauƙi da ci gaba ga mazauna yankin.
Al’ummar sun nuna fatan cewa ɗan majalisar zai duba koken nasu tare da ɗaukar matakin kammala aikin titin domin inganta rayuwar jama’a da bunƙasa ci gaban yankin.

