

Wasu daga cikin hotunan taron majalisin (Maulidin) takutaha, wanda Sayyada Hajiya Fatima Dala, tare da Sidiya Fadima Alawiyya Fagge suka shirya, kuma suka gabatar don nuna soyayya da farin ciki abisa samuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Manyan Malamai, Sharifai, Sha’irai ƴan siyasa da dubban masoya Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, sun halarci wannan taro mai albarka.
An gudanar da taron a Fagge, layin Alh Aliyu Hadejia, dake birnin kano.
Muna mik’a sak’on ban gajiya ga dukkan mahalarta wannan taron maulidi mai albarka, da fatan Allah ya ƙarar da rayuwar mu acikin soyayya da kaunar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

