
Ganduje ya Bayyana Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi da cewa wani gibi ne da zayyi wuyar cikewa.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace ya kadu a lokacin da ya sami labarin rasuwar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu da sanyin safiyar Ranar Alhamis bayan doguwar rashin lafiya.
Majiyoyin daga iyalin Marigayin sun ruwaito cewa ya rasu cikin kwanciyar hankali yana da shekaru sama da 100 a duniya
Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayyana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban mutum a fannin ilimin Musulunci wanda tasirinsa ya wuce tsararraki a tsakanin al’umma.
Ya ce sadaukarwarsa ta tsawon rai da ya samu wajena yaɗa ilimin Addinin Musulunci, tarbiyya da kyawawan ɗabi’a, da kuma jagorancin nagari ya sa ya sami girmamawa mai yawa a faɗin Najeriya da ma wasu Kasashen Duniya. Ta hanyar koyarwarsa, jagoranci, da tawali’u mai kyau, ya tsara rayuwa marasa adadi kuma ya ba da gudummawa sosai ga cigaban Addinin da al’ummar Musulmi baki Daya.
Tsohon Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Kuma Jagoran Jam’iyar a jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a madadin dukkan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano, yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ‘yan Darikar Tijjaniyya da kuma al’ummar jihar Bauchi, da kuma dukkan al’ummar musulmi a duniya.
Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya jikansa ya kuma bai wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa da mabiyansa da masoyansa juriyar jure wannan babban rashi.
ABK NAISA

