
Duk Dan Sandan Da Kukaga Yana Rakiyar Manyan Mutane Ku Kama Mana Shi — Cewar Shugaban ’Yan Sandan Najeriya
Sufeto Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa duk wani jami’in ‘yan sanda da aka gani yana rakiyar babban mutum ba bisa ƙa’ida ba, ya kamata a kama shi, domin an janye jami’an daga ayyukan gadin VIPs zuwa ayyukan tsaro na yau da kullum.
A yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja, Egbetokun ya tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda 11,566 da aka daura wa manyan mutane da wuraren tsaro na musamman a fadin kasar, yanzu an mayar da su cikin ayyukan sintiri domin karfafa tsaro. Wannan mataki na cikin umarnin shugaban kasa Bola Tinubu da aka bayar ranar 23 ga Nuwamba, 2025.
IGP din ya ce akwai wasu jita-jita da ake yadawa cewa jami’an ‘yan sanda sama da 120,000 ne ke ba da tsaro ga mutane masu kudi ko ‘yan siyasa, amma ya karyata hakan, yana mai cewa,
“Wadannan zarge-zargen karya ne. Ba mu da jami’an da yawansu ya kai wannan adadi a Najeriya. Umarnin shugaban kasa ya tabbatar cewa jami’ai 11,566 ne kawai ke kan irin wadannan ayyuka.”
Ya kara da cewa “Babu wani gwamna, aboki ko ‘yan uwa da za su iya matsa min lamba a kan wannan al’amari. Umurnin shugaban kasa ne, kuma zai tabbata an aiwatar da shi yadda ya dace.”
IGP Egbetokun ya ce mayar da jami’an zuwa ayyukan sintiri zai kara karfin rundunar musamman a wannan lokaci da ake fama da karancin ma’aikata, tare da kara ganuwar jami’an ‘yan sanda a wuraren da suka fi bukatar tsaro.
IGP Egbetokun ya yi kira ga ‘yan Najeriya su fahimci cewa rundunar na aiki tuƙuru wajen kare al’umma da kwato makamai, tare da tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda suna kan aiki inda ake bukatar su fiye da komai.
Source: DDL HAUSA

