
Abdulwahab Said Ahmad:
Maigirma Gwamna bisa girmamawa nake tura wannan sakon na halin da Hisba ta jihar Kano take ciki wanda takai ta kawo wasu naganin zasu iya yi mata kishiya, wannan yana da alaka da rashin kulawa da bangaren hisba yake fuskanta a halin yanzu.
Maigirma Gwamana bayan sabani da aka samu da shugabanta Malam Aminu Daurawa kayi musu alkawarin Sabbin Motoci na aiki, da karasa wasu gine gine dake hukamar amma zuwa yanzu shiru, alawus na dan hisba duk gimanshi inde ba kwamanda bane bai wuce N12,000 a wata wanda yake Local Government kuwa N9,500, idan an kirasu aiki ba bu isassun motocin zuwa idan kuma ansami motar babu kudin fetur dabadan wani bawan Allah dayake kawo faten wake ko taliya dakuma biredin dangote ba da wataran baifi mutun goma zaka riska a Shalkwata ba, wannan abuncin yasaka dayawan su sukan fito domin sun san akwai tallafi. Hakan yasa kowa ya raina Hisba don haka ake gani za a iya kafa sabuwa illa a canja mata suna.
ROKONA GA MAIGIRMA GWAMNA SHINE:
1. SAMAWA HISBAH MOTOCIN AIKIN A SHALKWATA DAKUMA KANANAN HUKUMOMI.
2. BASU KUDIN SAYEN MAI NA AIKI ISASSU.
3. KARA MUSU KUDIN ALAWUS DAGA N9,500 ZUWA N30,000 DUBA DA AIKIN DA SUKE.
4. GYARA MUSU OFISOSHIN SU MUSAMMAN WAYANDA SUKE KANANAN HUKUMOMI NA WAJEN KANO.
5. MUNA SAKE ROKON GWAMNA MAI ALBARKA DAKA BAWA DUKAN KWAMANDOJIN KANANAN HUKUMOMI KUJERAR AIKIN HAJJI DOMIN SAUKE FARALI KAMAR YADDA YAN MEDIA SUKAI A BARA.
6. YAWAN SAMAR MUSU DA HORO LOKUTA ZUWA LOKUTA
7. SAMAR DA OFISHIN MATA YAN HISBA A MANYAN KASUWANNIN DA MUKE DASU TARE DA MANYAN MAKARANTUN DOMIN TAKA RAWA WAJEN SETA AL’AMURA.
Abdulwahab Said Ahmad
annan yana daga cikin ce tasa kowa

