
Ana Zargin Cutar Kwalara
ta Kama Masu Garkuwa da Mutane a Zamfara.
A wata tattaunawa da jaridar Aminiya tayi da wani mutum mai suna Namadi Bawa ya bayyana yadda ya iske wasu masu garkuwa da mutane na fama da Amai da Gudawa lokacin daya kai kudin fansar dan uwansa da akai Garkuwa dashi.
Tunda fari, Namadi yace bayan masu garkuwa da mutanen sunyi garkuwa da dan uwan nasa akan hanyarsa ta dawowa daga Sokoto tare da neman kudin fansa, hakance tasa ya tashi zuwa jihar Zamfara domin kai wannan kudi.
Saidai bayan daya isa inda suka umarceshi kuma suka turo aka daukeshi zuwa cikin daji, ya iske da dama daga cikin masu garkuwa da mutanen cikin mawuyacin hali ga kuma alamomin cutar Amai da Gudawa.

