
Bashir Ahmad ya kankaro wa Najeriya mutunci a idon duniya daga barazanar Amurka, bayan caccakar wani makusancin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke ikirarin dole Najeriya ta soke shari’ar Musulunci da Hisbah.
Mai taimaka wa tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, ya yi wa Baamurken martanin cewa ‘ko giwa ta fadi, ta wuce Allah sarki’ ma’ana Najeriya cikakkiyar kasa ce mai cin gashin kanta.
Source: DW Hausa

