Abba Abdullahi

Idan aka ce a Kano akwai mutanen da suka zamo garkuwa ga marasa ƙarfi, ba za a manta da Alhaji Murtala Sule Garo ba. Ya kasance mai cike da kishin al’umma da kuma zuciyar taimako. A matsayin da Allah ya bashi a a baya, ya bar tarihin da za a rika dora misali a kai. Ya tallafa wa dubban mata da hanyoyin arziki, ya taimaka wa matasa wajen kafa sana’o’i, kuma ya kasance mai bude kofofi ga kowane irin bukata. Kowa ya sani yanzu ba shi da mukami amma mutane suna ci gaba da samun tallafi daga gareshi a koda yaushe. Wannan halin nashi ya tabbatar da cewa gaskiya tana da wurin zama a zuciyar sa. Fatanmu shi ne Allah Ya daukaka shi, Ya ba shi babban mukami a gwamnatin tarayya domin amfani da nagartarsa a doron Kasa, domin da ace Kwamanda yana da muƙami a yanzu, da tuni matasa da yawa sunyi arziki a jihar kano.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

