
Aikin Taimakon Jama’a da DG NPC Dan Agundi da ED REA Eng. Umar Ganduje suke yi yana kamanceceniya
Zamu cigaba da Sauke nauyin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya Dora mana na Taimakon al’uma – Injiniya Umar Abdullahi Umar Ganduje
Babban Daraktan Zartarwa a Hukumar samar da hasken wutar Lantarki na Kasa ya sake Jaddada kudurin Gwamnatin Tarayya na inganta rayuwar al’uma tun daga tushe.
Daraktan Zartarwar Hukumar Injiniya Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayani a wajan taron bayar da tallafi ga ‘Yayan Jam’iyar APC na yankin Kananan Hukumomin Rimin Gado da Tofa da Dawakin Tofa a jihar Kano.
Injiniya Umar Yace a cikin wattani shida da bashi Mikamin Daraktan Gudanarwa a Hukumar REA ya bayar da irin wadannan tallafi a matakai daban daban har karo shida domin dai tallafawa al’umar yankin Nazabar tasa ta Rimin Gado da Tofa da Dawakin Tofa.
Inda yace wannan shiri zai cigaba dayinsa daga lokaci zuwa lokaci domin dai al’umar yankin nasa Susan cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta banbanta da sauran.
Da yake jawabi ga wadanda suka dawo Jam’iyar APC kuwa daga Jam’iyar NNPP Injiniya Umar Ganduje Yace suma baza’a Barau a baya ba wajan cin gajiyar irin wannan tallafi, nan gaba Kadan za’a basu nasu rabon kamar yadda aka bawa sauran.
Yace ko shakka Babu zasu cigaba dayin koyi ga magabata ta hanyar kyautatawa al’umarsu.
A nasa jawabin Babban Daraktan Hukumar NPC, Dr. Baffa Babba Dan Agundi taya injiya Umar Abdullahi Ganduje murna yayi akan yadda yake sauke nauyin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya Dora masa
Baffa Babba Yace injiya Umar Yana daga cikin wadanda suka sami mukami ‘yan asalin jihar Kano Kuma yake taimakon ‘yan Jam’iyar APC anan jihar Kano musamman ma daga yankin da ya fito na Dawakin Tofa da Tofa da kuma Rimin Gado a nan jihar Kano.

