
Zaku iya tsayuwar Arfat a gidajen ku kamar yadda yazo a Hadisin Manzon Allah SallAllahu Alaihi Wasallam
Hadith
An samo daga *Jabir* (Allah Ya kara yarda a gare shi) yace, *Manzon Allah (SAW)* yace; babu wani mutum Musulmi da zai tsaya a ranar *Arfat* idan baya filin *Arfat* ya samu wani wuri ya fuskanci *Al-Qibla* ya zauna sai ya karanta wadan nan kamar haka:-
– *La’ilaha illahu Wahadahu Lashari Kalahu Lahulmulku Wa Lahulmulku Wa huwa Ala Kulli Shai’un Qadir* – 100×
– *Suratul Iklas (Qul HuwalAllhu Ahad)*- 100×
– *Allahumma Salli Ala Muhammad Wa’ala Ali Muhammad Kama Sallaita Ala Ibrahim Wa’ala Ali Ibrahim Innaka Himidun Majid, Wa’alaina Ma’ahum* – 100×
Babu wanda zai yi wannan sai *Allah (SWA) Ya* tara *Mala’ikun Sa Yace* me kuke ganin ya kamata *Na* saka ma wannan bawan *Nawa?*
Sai *Mala’iku* suyi shiru, don babu wanda zai iya magana
Sai *Allah Yace* wannan bawan *Nawa* ya *Tsarkake Ni,* yace *La’ilaha illah* ya *Girmama Ni* ya *Daraja Ni* ya nuna ya san *Ni* kuma ya *Yabe Ni* sannan ya yima *Annabi Na* Salati
Sai *Allah Yace* toh ku zama shaida *Na* gafarta mashi zunuban shi duka sannan *Na* bashi ceton kan shi.
Da zai bukaci *Na* bashi ceto da *Na* bashi ceton duk wanda ke filin *Arfat* din nan
Daga nan sai bawa ya roki duk abunda yake so *Allah Ta’ala Zai* bashi
*Allah Ya* bamu ikon yi *Ya* gafarta mana *Ya* kuma biya mana dukkan bukatun mu na alkhairi, ameeeeen thumma ameeeeen

