
A karamar hukumar Rano Daliban makarantun firamare sama da dubu goma sha uku da dari bakwai da saba’in da takwas ne ake sa ran za su amfana da kayan sawa na makaranta.
Shugaban karamar hukumar ta Rano, Malam Naziru Muhammad Ya’u Rano ne ya bayyana haka ya yin kaddamar da mika bandiran yadin ga telolin yankin wadanda za su yi aikin wanda aka yi a dakin taron sakatariyar karamar hukumar ta Rano.
Wannan na cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in shiyar yada labarai ta Rano, Abdullahi Musa Gyadi Gyadi ya rabawa manema labarai, inda sanarwar ta kara da cewa,Malam Naziru Muhammad Ya’u Rano ya kara bayyana cewa, a baya gwamnatin jihar Kano ce ta ke yin aiki dinkin kayan makarantar daliban amma yanzu ta baiwa kananan hukumomi dama don su je su baiwa telolin yankunan su aikin don su ma su amfana.
Shugaban karamar hukumar yace duba da kalolin yadikan da za a dinka, kalolin fari ne da kore amma saboda a karamar hukumar da akwai wasu makarantun da dama daliban su suke amfani da kaloli daban-daban, majalisar karamar hukumar ta tanadi wasu kalolin yadikan daban daban na dubban naira don dinkawa daliban wadancan makarantun a yankin.
Ya bada tabbacin cewar, karamar hukumar a shirye ta ke don ci gaba da koyi da gwamnatin jihar don bunkasa fannin ilmi a yankin.
Ya kuma bukaci al’umar karamar hukumar da su kara yiwa gwamnatin jiha da karamar hukumar addu’o’i don kara bujiro da ayyukan bunkasa yankin.
Sakataren ilmi na karamar hukumar, Alhaji Sani Yaro Ibrahim ya nuna gamsuwa da ayyukan da gwamnatin jihar Kano dama karamar hukumar suke yi don inganta ilmi a yankin.
Alhaji Sani Yaro Ibrahim ya roki tailolin da za su dinka kayan makarantar su yi aikin su bisa gaskiya da rikon amana wajen yin dinki mai inganci don daliban su dade suna amfana da kayan.
Sa hannu,
Abdullahi Musa Gyadi Gyadi
Jami’in shiyar yada labarai mai lura da shiyar Rano.

