
Shugaba Bola Tinubu ya karɓi bakuncin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Asabar, bayan dawowar Jonathan Najeriya daga ƙasar Guinea-Bissau.
Jonathan ya je ƙasar ta Yammacin Afirka ne a wani aikin sa ido kan zaɓe inda bayan zaɓen aka samu damuwa game da tsaron lafiyarsa sakamakon kifar da gwamnatin kasar da sojoji suka yi.

