
Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta tabbatar da gano sababbin nau’o’i guda huɗu na ƙwayar cutar shan inna a jihar, tare da gargaɗin cewa idan ba a ci gaba da yin rigakafin yadda ya kamata ba, kwayar cutar na iya sake yaɗuwa bayan an kawar da ita.
Farfesa Salisu Ahmad, wanda Daraktan hukumar ya wakilta ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da jama’a domin tunawa da Ranar Polio ta Duniya a Kano, a ranar Laraba.
Ya ce tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, Kano ce cibiyar yaɗuwar cutar a Najeriya, amma sakamakon hadin gwiwar gwamnatin jihar da abokan hulɗa, an samu nasarar kawar da ita.
Sai dai ya bayyana cewa aikin bai ƙare ba, domin an sake gano sababbin nau’o’i hudu na ƙwayar cutar, inda har yanzu ana binciken ɗaya daga cikinsu a ɗakin gwaj
e-gwaje.

