
ADC ta rusa shugabancin jam’iyyar na Kano tare da kafa kwamitin riƙo
Jam’iyyar ADC ta rusa shugabancin ta na Jihar Kano tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai jagoranci harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaɓen shugabanni.
Mataimakiyar shugabar ADC ta ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Najaatu Muhammad, ce ta sanar da hakan a ranar Litinin yayin taron manema labarai a Kano.
Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Kama Motoci 81 Marasa Lamba da Wadanda Ake Rufe Lambobinsu
Najaatu ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma ba don nuna fifikon wata ɓangare ba ne, sai dai domin dawo da daidaito, tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin jam’iyyar, da kuma cike giɓin shugabanci da ya taso a jihar.
Ta kuma yabawa mambobin ADC a Kano kan gudummawar da suka bayar wajen gina jam’iyyar, tana mai tabbatar da cewa shugabancin ƙasa na jam’iyyar na daraja jajircewarsu da sadaukarwar da suka yi.

