
WATA SABUWA: An kewaye dazukan da Yan bindiga su sace Yan matan Jihar Kebbi. Inji Babban Hafsan sojin kasa.
Babban hafsan sojin kasar Najeriya, Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa
Ana samun ci gaba wajen ceto daliban mata 25 da aka sace a Jihar Kebbi. An kewaye babban yankin, kuma ana sa ran samun wasu labarai nan ba da jimawa ba.
Babban Hafsan Sojin Kasa ya yi wannan bayani ne bayan ganawar da ya yi da Shugaba Tinubu tare da sauran manyan hafsoshin sojoji.

