
Kaduna: ’Yanbindiga sun sace babban limami da jagoran Fulani a Kagarko
’Yanbindiga sun sace babban limamin masallacin Janjala Central, Malam Bello Abdullahi, da jagoran Fulani na yankin, Shehu Bello, tare da wata mata, a yayin hare-haren da suka kai wasu yankuna a karamar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Harin, wanda ya faru a daren Talata, ya shafi kauyuka da suka hada da Iddo, Gidan-Makeri, Kohoto da Janjala, inda maharan suka kuma kwashi shanu tare da tilasta wa mazauna yankunan da dama guduwa.
Mazauna yankunan sun ce lamarin ya jefa yankin cikin tsoro, lamarin da ya sa mutane da yawa suka tsere zuwa Kagarko da Sabon-Wuse. Sun kara da cewa harin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da ’yan bindiga suka bayar na neman kudin fansa ₦6m kan wasu mutanen da aka sace a baya.
Har zuwa lokacin hada rahoton, ba a samu wata sanarwa daga rundunar ’yansandan jihar ko gwamnatin Kaduna ba, yayin da mazauna yankunan ke rokon gwamnati da ta kara tsaurara tsaro da kuma tabbatar da sakin wadanda aka sace.

