
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ayyana hutu a yau Juma’a domin girmama rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a jiya Alhamis.
A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, an bayyana cewa hutun zai bai wa ma’aikata, ɗalibai da al’ummar jihar dama su halarci jana’izar marigayin.
A cewar sanarwar, za a gudanar da sallar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi a yau Juma’a a filin Idi da ke cikin birnin Bauchi, kafin a kai gawar marigayin a binne a masallacin Juma’arsa.
Tun daga daren jiya ake ci gaba da ganin dubban al’umma daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje na tururuwa zuwa jihar domin halartar jana’izar. Haka kuma al’ummar Bauchi na cigaba da taruwa a wurin da za a gudanar da sallar, domin girmama fitaccen malamin da ya shafe shekaru yana hidimar addini.

