
Innalillahi wainna ilaihir rajiuunn, Fitacccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu a cikin daren da ya gabata, kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar wa RFI Hausa. Majiyar ta ce za a gudanar da jana’izarsa a gobe Juma’a a garin Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh. Allah ya yi masa rahama

