
Gwamna Bago Ya Gano Masu Taimakawa ‘Yan Bindiga wajen Kaiwa Makarantu Farmaki.
Gwamnan jihar Neja Muhammad Umaru Bago, ya kai ziyarar jaje fadar Sarkin Borgu kan daliban da ‘yan bindiga suka sace.
Umar Bago ya bayyana cewa akwai maau taimakawa ‘yan bindiga wajen kai hare-haren da suke kai wa a jihar.
Gwamna Bago ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na bakin kokari domin ganin an kubutar da daliban cikin aminci.
Gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya ce masu bada bayanai (infomomi) na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa ’yan ta’adda damar kai hare-hare. Gwamna Bago ya nemi a ɗauki tsauraran matakai a kansu domin rage matsalar tsaro a jihar.
Jaridar The Guardian ta ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin ziyarar jaje da ya kai fadakar Sarkin Borgu. Gwamna Bago ya je ziyarar jaje Gwamna Bago ya jagoranci tawaga daga jihar domin jajantawa kan harin da ya kai ga sace daliban makarantar St. Mary’s Catholic School, Papiri, da ke karamar hukumar Agwara.
Bago ya bayyana cewa jami’an tsaro tare da gwamnatin jihar na kokari matuka domin ganin an ceto daliban cikin gaggawa. Ya bukaci jama’a su rika bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro, tare da jan kunnen al’umma kan nuna kiyayyar addini.
Gwamna Bago ya bayyana cewa zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummomi na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro.
Sarkin Borgu ya gode wa gwamnan bisa ziyarar, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai kula da jin daɗin mutanensa. Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ’yan bindiga suka mamaye gandun dajin Borgu, inda ya roki gwamnati ta tarayya da ta jiha su tserar da yankin daga hannun miyagu.
Tun da farko, karamin ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa saurin daukar matakai kan lamarin.

