
Ministan harkokin wajen Ƙasar nan , Yusuf Maitama Tuggar ya yi watsi da gargaɗin Shugaba Trump na ɗaukar matakin soji kan Najeriya.
Da yake jawabi a taron manema labarai da ya gudanar a birnin Berlin tare da takwaransa na Jamus, Mista Tuggar ya ce Najeriya na bayar da ƴancin addini tare da aiki bisa doron doka.
Yusuf Tugga Yace Kundin tsarin Mulkin Najeriya da dokokin ƙasar sun haramta cin zarafin addini tare da bayar da damar ƴancin gudanar da addini”, in ji shi.
”Babu yadda za a yi gwamnatin Najeriya ta goyi bayan ta kowane fanni na yadda za a ci zarafin mabiya wani addini”, in ji Tuggar.
Mikiya Hausa Times ta ruwaito Ministan harkokin wajen na cewa gwamnatin ƙasar ba za ta yarda a mayar da ƙasar tamkar Sudan ba.
Ya kara da cewa ‘Abin da muke so duniya ta fahimta shi ne ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin, Najeriya na da yawan al’umma fiye da miliyan 230, ƙasar da ta fi kowace yawan jama’a da ƙarfin dimokraɗiyya a Afirka”, a cewarsa.

