
Mun shirya, wannan lokacin za mu fito Hawan Babbar Sallah — Sarkin Kano Bayero
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado-Bayero CFR, CNOL, JP, ya ce tuni sun kammala shirin su na hawan babbar sallahr bana kamar yadda aka saba gudanarwa a bisa al’ada.
Sarkin Kano Bayero, ya bayyana hakan ne a yau Litinin, yayin da ya ke karɓar baƙuncin gamayyar shugabannin ƙungoyi 200 masoya da magoya bayan sa a fadar sa dake gidan Nasarawa Kano.
A jawabin sa, shugaban gamayyar ƙungiyoyin masoya sarkin Kano Aminu Ado-Bayero, wato Muhammad Fagge, ya ce sun zo fadar sarkin ne domin su ƙara jaddada mubaya’ar su — tare da roƙon mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado-Bayero ya taimaka wannan lokacin ya fito don gudanar da haye-hayen sallah.
“Allah ya taimaki sarki, dubban miliyoyin masoyan ka mata, maza, tsofaffi da yara su na cikin tsananin damuwa sakamakon rashin gudanar da haye-hayen sallah da ba’a yi.” Inji Muhammad Fagge.
Muhammad Fagge, ya kuma ƙara da cewa “Gamayyar ƙungiyoyi 200 ba ma tare da duk shugaban da baya tare da mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado-Bayero kuma yake neman tozarta shi, ko ya ke ƙoƙarin sai ya ƙwace masa sarautar da ya gada a wajen mahaifin sa.”
Da yake maida amsa ga kalaman shugaban gamayyar ƙungiyoyin masoyan sa 200 na jihar Kano, mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado-Bayero CFR, CNOL, JP ya ce “Mun shirya, wannan lokaci za mu fito kuma za mu yi Hawan babbar sallah da zarar hukumomin da mu ka turawa takardun hawa sun sahhale ma na — domin mu ma su bin doka ne.” In ji sarkin Kano Alhaji Aminu Ado-Bayero.

