
Kwankwasiyya ta yi watsi da kiran da gwamnatin Kano ta yi wa mataimakin gwamna da ya ajiye mukaminsa
Kungiyar Kwankwasiyya ta yi Allah-wadai da kiran da gwamnatin jihar Kano ta yi na neman Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi murabus, tana mai bayyana matakin a matsayin tsokana da rashin godiya.
A wata sanarwa da kakakinta, Hon. Habibu Saleh Mailemo, ya fitar, kungiyar ta ce kiran bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiya da jituwa a harkokin siyasa a jihar.
Ta zargi wasu jami’an gwamnati da yunkurin wulakanta magoya bayan jagoranta, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ke cikin gwamnati.
Kwankwasiyya ta jaddada cewa Mataimakin Gwamnan an zabe shi ne tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a tikitin hadin gwiwa, don haka huruminsa ya fito ne daga kundin tsarin mulki da kuri’un jama’a, ba daga ra’ayin wani mutum ba.
Kungiyar ta ce gwamnatin Kano samfurin gwagwarmayar Kwankwasiyya ce, tare da gargadin cewa ba za ta yi shiru ba idan aka ci gaba da wulakanta mambobinta.

