
Daga Sadiq Abubakar
Rundunar Hizbah ta Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa ta gargadi cewa za ta cafke duk wanda aka samu da aikata ko yada badala a yayin bukukuwan Maulidi.
Mataimakinsa ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsafta da kiyaye dokokin addini, tare da jan hankalin masu karya doka cewa za su fuskanci hukunci.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su gudanar da Maulidi cikin natsuwa, tare da bin dokokin gwamnati da na addini domin kaucewa tashin hankali.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko abknaisa100@yahoo.com

