
Bayo Onanuga, mai ba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai, ya yi kakkausar suka ga Kabiru Tanimu Turaki, shugaban wani bangare na jam’iyyar PDP.
A ranar Talata, Turaki ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya tsoma baki a rikicin da ke ci gaba tsakanin bangarorin jam’iyyar PDP.
Onanuga ya bayyana wannan kira a matsayin abin ƙyama da kuma babban laifi na cin amanar ƙasa, yana mai cewa wannan abin da Turaki ya aikata “ba zai taɓa gogewa ba a tarihin siyasar Najeriya.”
Ya ce “Ba za mu taɓa mantawa da wannan bidiyon ba, ranar da wani ɗan siyasa a Najeriya ya nemi a yi wa ƙasarmu katsalandan daga ƙasar waje, duk saboda rikicin cikin jam’iyyarsu.”

