
YANZU-YANZU: An Bawa Hammata Iska A Hedikwatar Jam’iyyar PDP a Abuja.
Rahotanni daga hedikwatar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke Wadata House sun bayyana cewa fadan ya barke tsakanin wasu ‘ya’yan jam’iyyar a yau.
Har yanzu ba a bayyana musabbabin barkewar fadan ba, amma ganau sun ce rikicin ya fara ne yayin da ake jiran fara wani muhimmin taron jam’iyyar. Jami’an tsaro na kokarin shawo kan lamarin domin hana rikicin yaduwa. Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani.
📷- Trust Radio

