
ABIN YABA: Yadda Jarumin Jami’in Tsaro Ya Hana Afkuwar Kashe Kai A Masallacin Harami
An hana afkuwar wani mummunan lamari a Masallacin Harami da ke Makka a ranar Alhamis, bayan da wani mutum ya yi yunƙurin jefa kansa daga wani bene na sama. Jami’an tsaron Masallacin sun kai ɗauki cikin gaggawa, lamarin da ya hana aukuwar bala’i tare da tayar da hankalin masu ibada.
A yayin aikin ceton, wani jarumin jami’in tsaro mai suna Rayan Al-Asiri ya sadaukar da kansa domin hana mutumin faɗuwa, inda ya samu raunuka. An garzaya da shi asibiti, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa jikin nasa yana kyau, yayin da hukumomin Saudiyya suka yaba masa bisa jarumta da jajircewarsa wajen kare rayukan masu ibada a wurin mai tsarki.

