Daga Ayman Ado:

Wadannan Hotunan na nuni da yadda Gada guda daya tilo da mutanen garin “Yanshana dake Karamar Hukumar kumbotso a Jihar Kano suke amfani da ita wajen shige da fice a garin, gadar dai ta karye ne a sanadin daminar wannan shekara.
Idan har Babban gari irin wannan dake cikin birnin kano zai rasa samun daukin Gwamnati cikin karamin lokacin, me kuke tunani Kuma ace a wajen garin kano haka ta faru ?
Saboda yanke tsammani daga al’ummar wancan gari na “Yanshana, Sai yan garin ne suka hada kudi suka yi gadar wucingadi wato (temporary) gada ta katako domin su cigaba da rayuwa.
Ya kamata dai mahukunta su duba su ceto rasuwar al’umar wannan yanki, Kuma shugabanni su dunga tunawa da amanar da Allah ya Dora musu ta kare rayuka da dokiyoyin al’umar da suke mulka Domin Allah zai tambayesu irin yadda suka tafiyar da amanar al’umar da Allah ya damka musu.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

