
Sarkin Musulmi Ya NemI A Shigar Da Sarakuna Cikin Tsarin Albashi N70,000
Sarkin Musulmi, Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci gwamnatin Jihar Sokoto da ta shigar da sarakunan gargajiya cikin tsarin biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar.
An gabatar da wannan buƙata ne ta hannun Hakimin Wurno, Sarkin Sudan Alhaji Kabiru Ci Gari Alhassan, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi a yayin taron tattaunawa da al’umma da Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Jihar Sokoto ta shirya, domin shirye-shiryen gabatar da kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026.
A cewar wakilinsa, Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin taka rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da haɗin kai a tsakanin al’umma, tare da neman a mutunta rawar da suke takawa ta hanyar shigar da su cikin tsarin albashi na sabon mafi ƙarancin albashi.
Sai dai kuma, wasu daga cikin al’umma na ganin cewa a irin wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar, musamman sace-sace da barazanar hare-hare da al’ummar Musulmi ke fuskanta, ana sa ran shugabanni na gargajiya su bayyana matsayinsu a fili kan irin waɗannan matsaloli, kodayake babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar Sarkin Musulmi dangane da wannan batu a yayin taron.

