WASU DALIBAN JAMI’AR NORTHWEST “YAN KARAMAR HUKUMAR BIRNIN KANO SUNA GAB DA RASA KARATUNSU SABODA RASHIN CIKA MUSU ALKAWARIN DA “YAN SIYASA SUKAYI MUSU.

Dalibai daga karamar hukumar Birni a jami’ar Northwest University Kano suna neman su rasa gurbin karatun su bayan rashin cika masu alkawari da yan siyasa su kayi masu
Daliban jami’ar Northwest University Kano daga suka fito daga ƙaramar hukumar Birni na fuskantar barazanar rasa cigaban karatunsu, bayan da suka kasa samun tallafin biyan kuɗin makaranta duk kuwa da alƙawuran da aka yi musu.
A baya, ɗaliban sun samu tabbacin taimako daga ɗan majalisar tarayya na yankin, Hon. Sagir Ƙoƙi, wanda daga bisani ya sanar da cewa ba zai iya biya musu kuɗin ba. Haka zalika, sun nemi tallafi daga tsohon ɗan majalisa Hon. Sarki Aliyu Daneji, amma shima ya gaza.
Kakakin ƙungiyar ɗaliban ya ce har ma shugaban ƙaramar hukumar Birni, Hon. Sleem Hasheem, ya kasa ɗaukar nauyin biyan, duk kuwa da irin matsanancin halin da ɗaliban suke ciki.
Yanzu haka dai hukumar makaranta ta sanya ranar Lahadi a matsayin ƙarshe da za a karɓi kuɗin, lamarin da ya jefa ɗaliban cikin tsananin fargaba, musamman ganin da dama daga cikinsu mata ne masu ƙaramin ƙarfi waɗanda iyayensu ba su da ikon ɗaukar nauyin kuɗaɗen.
Ƙungiyar ɗaliban ta roƙi gwamnatin Jihar Kano da sauran masu hannu da shuni su ɗauki mataki cikin gaggawa, domin kare makomar waɗannan dalibai. Kakakin ƙungiyar ya ce, “Idan ba a taimaka ba, akwai yiwuwar mu rasa damar ci gaba da karatu, wanda hakan na iya zama babban koma baya ga makomar rayuwarmu.”
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 09099222211 ko abkny

