
TIRKASHI: Nicki Minaj za ta yi jawabi a UN kan tsanantawa da hare-haren Kiristoci a Najeriya
Shahararriyar mawakiya ta duniya, Nicki Minaj, za ta yi jawabi a wani taro na Majalisar Dinkin Duniya (UN), inda za ta mayar da hankali kan al’amarin tsanantawa da ake yi wa Kiristoci a Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, mawakiya za ta yi wannan jawabi ne tare da wasu jami’an Amurka, don jawo hankalin duniya kan hare-haren ‘yan jihadi da ake kaiwa al’ummar Kiristoci a Najeriya.
An ce Minaj za ta bayyana yadda irin wannan tsanantawa da tashin hankali ke shafar rayuwar Kiristoci, tare da kiran duniya da ta dauki matakan kare rayuka da hakkokin mutane a wannan yanki. Wannan jawabi na Nicki Minaj zai zo ne a daidai lokacin da ake ta kara samun rahotanni na hare-hare kan Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya, inda ake samun rashin tsaro da garkuwa da mutane.
Masu sharhi na ganin wannan mataki na Minaj zai taimaka wajen jawo hankalin duniya da hukumomin kasa da kasa, musamman ma Majalisar Dinkin Duniya, don a dauki matakan kare rayukan al’umma da kuma kawo karshen tashin hankali a Najeriya.

