Shugabannin Matasan APC Uku Sun Rasu a Hatsarin Mota Zuwa Taron Jam’iyya
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu shugabannin matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) guda uku daga Ogbadibo a Jihar Benue State sun rasu a wani hatsarin mota.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar Makurdi zuwa Lafia yayin da suke kan hanyarsu ta halartar wani taron jam’iyyar APC.
Majiyoyi sun ce sauran mutanen da ke tare da su a cikin motar sun samu raunuka, inda ake ci gaba da kula da su a asibiti.
Wannan lamari ya jawo alhini a tsakanin ‘yan jam’iyya da al’ummar yankin.
Allah Ya jikansu da rahama, Ya ba iyalansu haƙuri. Ameen.

