BY MUSADDIQ WADA WAZIRI

SHUGABANCI DA RIKON MULKI CIKIN DAIDAITO
Idan Allah ya baka matsayin jagoranci a cikin al’umma kada ka bari iko da isa su rinjaye ka. Shugabanci ba lasisin raina jama’a ba ne; dama ce ta nuna tausayi, adalci da mutuntawa ga wanda kake jagoranta da abokan aiki.
Cikakken shugaba shi ne wanda yake samar da yanayi na kwanciyar hankali, inda mutane suke jin suna da daraja, tsaro, da walwala a gaban sa. Ka tambayi kanka: shin mutane suna jin aminci da mutunci idan suna tare da kai?
Ka tuna, izza ba ita ce take zama sakamakon shugabanci ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne jagorancin da zai sauya rayuwa, wato wanda zai iya zaburar da mutane, ya karfafa musu gwiwa, ya motsa su, suyi kirkira da kawo sauye-sauye da za su taimaka wajen gina nasarar rukunin al’ummar da kake shugabanta
Yayin da kake kokarin nuna kwarewar ka ta shugabanci, ka rungumi tawali’u da kan-kan da kai wajen yunkurin kawo cigaba. Wannan na taimakawa mutum ya tashi da karfi ba tare da girman kai ko jin isa ba.
Ka fahimci bambanci tsakanin alfahari na gaskiya (¹wanda ke fitowa daga hakikanin nasara) da alfahari na girman kai (²wanda yake cike da girman kai da raini). Na farkon yana gina mutum, na biyun yana rusa shi.
Kar ka yi watsi da abin da mutane ke fada maka a matsayin ra’ayi, fahimtar su ko tsokaci. Ka dauke shi a matsayin damar koyo da yin tunani, domin sau da yawa sauraron fahimtar al’umma akan al’amura yana nuna wuraren da ake bukatar kayi gyara don ka kara zama shugaba nagari.
A kowane hali, kar ka tauye mutuncin abokan tarayyar ka. Rayuwa juyi-juyi ce, kuma kowa na iya fuskantar canji. Ma’aunin nagartaccen shugaba ba yawan iko ko izzar da yake dashi ba ne, illa irin mutuncin da yake karewa na mutanen sa.
#MatasaMadogara
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko abknaisa100@yahoo.com

