
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa shekarar 2026 za ta bude sabon babi na karuwar tattalin arziki mai karfi, inda gwamnatinsa za ta kara rage hauhawar farashi.
A sakon sabuwar shekara da ya aikewa ’yan kasa, Tinubu ya ce yana da kwarin gwiwa cewa hadin kan al’umma zai sa shekarar ta zama ma fi alheri.
Ya bayyana cewa a 2025, Gwamnatinsa ta aiwatar da manyan gyare-gyaren tattalin arziki, ta sake daidaita harkokin kudi, kuma ta samu ci gaba.

